(ABNA24.com) Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya zargi ‘yan jam’iyyar Democrat da cewa su ‘yan leken asiri ne.
A cikin wani bayanin da ya saka a shafinsa na twitter, Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya zargi ‘yan jam’iyyar Democrat da cewa suna yin aikin leken asiri a kansa, haka nan kuma suna yin zagon kasa ga zaben shekara ta 2020 mai zuwa.
Ya ce hakkinsa ne ya san wanda ya yi masa leken asiri, domin bin kadun tattaunawarsa da wasu manyan shugabannin kasashen duniya ya sabawa ka’ida da doka, saboda haka yana son sanin mutumin da yabi kadun maganganunsa ta wayar tarho.
Trump dai yana fuskantar gagarumar matsala, tun bayan bankado wasu bayanan sirri danagne da tattaunawar da ya yi da shugaban kasar Ukraine, inda ya bukaci shugaban an Ukraine da gudanar da bincike kan batun wata kwangila da dan Joe Biden ya yi a kasar.
‘Yan majlaisar wakilan Amurka daga jam’iyyar Democrat sun zargi Trump da neman shigo da wasu bangarori daga wajen da su katsalandana a cikin harkokin zaben kasar, wanda hakan yasa a halin yanzu yake fuskantar barazanar tsigewa.
/129
1 Oktoba 2019 - 04:40
Lambar labari: 979458
Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya zargi ‘yan jam’iyyar Democrat da cewa su ‘yan leken asiri ne.